A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron bainar jama'a na gaggawa game da batun kasar Syria, inda Liu Jieyi ya nuna cewa, kwanan baya, an ci gaba da fuskantar rikice-rikice a wasu sassan kasar Syria, lamarin da ya janyo hankalin kasar Sin kwarai da gaske. A halin yanzu, ya kamata gamayyar kasa da kasa su dukufa a fannoni guda hudu domin warware matsalar kasar Syria yadda ya kamata, watau cimma burin tsagaita bude wuta a kasar, yin shawarwarin siyasa, samar da taimakon jin kai da kuma yin hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.
Kaza lika ya ce, ya kamata a ci gaba da nuna goyon baya ga manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria, kana a gaggauta farfado da shawarwarin neman sulhu na Geneva, ta yadda za a warware matsalar kasar Syria bisa bukatun al'ummomin kasar Syria, da kuma kiyaye moriyar bangarori daban daban da abin ya shafa yadda ya kamata. Kana, ya kamata kasashen dake yankin su taimaka cikin himma da kwazo wajen inganta ayyukan warware matsalar Syria ta hanyar siyasa.
Bugu da kari, Liu Jieyi ya ce, kasar Sin tana son ci gaba da samar da taimako domin warware matsalar kasar Syria a dukkan fannoni ta hanyar nuna adalci kuma yadda ya kamata. (Maryam)