A jiya Talata gwamnatin Najeriya ta sha alwashin takaita ayyukan tsagerun yankin Niger Delta da kashi 80 cikin 100, inda gwamnatin za ta gina ofisoshin 'yan sanda a cikin teku.
Sifeto janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya fada a Abuja cewar, za'a samar da kwalejin nazarin harkokin teku a yankin Bayelsa mai arzikin mai wacce za ta kunshe ofisoshin 'yan sanda domin a samu damar gudanar da ayyuka cikin sauki.
Idris ya fada cewa, za'a horas da jami'an rundunar tsaro ta musamman mai yaki da 'yan fashi tare da hadin gwiwar kungiyar lauyoyi ta kasa, da gamayyar kungiyoyin fararen hula, da kuma kungiyar kare hakkin bil'Adama.
Babban sifeton 'yan sandan ya bayyana hakan ne kimanin sa'o'i 24 bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da manufofin mayakan tsagerun yankin Niger Delta na yunkurin rugurguza tattallin arzkin kasar.
Ya kara da cewa, tsagerun na neman durkusar da tattalin arzikin Najeriyar, sai dai shugaba Buhari ya ce, suna kokarin tattaunawa da shugabannin mayakan domin shawo kan matsalar.
Ya ce, al'amarin tsagerun yankin Niger Delta batu ne mai sarkakkiya, ba su da takamamman tsarin shugabanci, sai dai shugaban Najeriyar ya yi alkawarin lalubo bakin zaren warware matsalar nan gaba ba da jimawa ba. (Ahmad)