in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu akwai koma baya ga shirin raya tattalin arziki bisa ruwan teku a Afrika
2016-10-14 10:59:35 cri
A jiya Alhamis shugabar zartarwar kungiyar tarayyar Afrika ta koka game da yadda kasashen Afrika ke tafiyar hawainiya wajen bunkasa tattalin arziki bisa ruwan teku, duk da irin dunbun albarkatun dake jibge a nahiyar.

Nkosazana Dlamini Zuma, ta fadi hakan ne cikin wani jawabi ga taron shugabannin kungiyar kan samar da bunkasuwa da tsaron teku a Afrika wanda aka gudanar a Lome babban birnin kasar Togo.

Madam Zuma, tace duka duka bai wuce kashi 1.8 na ma'aikatan jiragen ruwan duniya'yan Afrika ne, a yayin da kashi 90 cikin 100 na shigi da ficin hajojin nahiyar ana gudanar dashi ne ta ruwa.

Madam Zuma tace duk da cewar ana gudanar da sufurin kayayyaki ta tekunan kasashen Afrika, amma sam kasashen ba sa cin gajiyar hada hadar, ciki harda batun rashin samar da ayyukan yi.

An kiyasta za'a iya samun arziki ta hanyar amfani ayyukan tattalin arzikin ta hanyar teku na sama da dalar Amurka trilliyan daya, sannan za'a samar da dubban guraben aikin yi ga matasan nahiyar ta Afrika,.

Dlamini Zuma, ta bayyana cewa an tsara shirin raya tekunan Afrika nan da shekarar 2050 inda ake saran al'ummun nahiyar za su ci gajiyar tekuna da koguna da ke nahiyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China