in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 1.3 suna fama da karancin abinci a Kenya
2016-10-16 13:30:59 cri
A jiya Asabar 15 ga wata, babbar jaridar Kenya, Daily Nation ta ba da labarin cewa, kimanin mutane miliyan 1.3 ne suke fuskantar barazanar karancin abinci a kasar sabo da bala'in fari.

Labarin ya ce, yanzu jihohi 23 na Kenya suna fama da bala'in fari.

A daren ranar Jumma'a 14 ga wata, ministan raba iko da tsara shiri na Kenya Mwangi Kiunjuri ya bayyana wa kafofin yada labarai a birnin Nairobi, hedkwatar kasar cewa, kawo yanzu babu rahoto dangane da mutuwar mutane sakamakon karancin abinci. Ya ce, gwamnatin kasar ta dauki alkawarin cewa, tana kokarin shawo kan matsalar cikin gaggawa, za ta ba da agaji ga wadanda suke cikin tsananin bukata cikin lokaci.

Minista Mwangi Kiunjuri ya bayyana cewa, yanayin karancin abinci ya sami kyautatuwa sosai a shekarar bana, idan aka kwatanta bisa ga barazanar da aka fuskanta a bara inda mutane miliyan 2.5 ne suka yi fama da karancin abinci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China