in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun CAD ya kafa reshensa a kasar Kenya
2016-09-23 10:50:58 cri
Asusun ci gaban Sin da Afirka (CAD fund) ya kafa wani reshensa a kasar Kenya a ranar Alhamis, da nufin taimakawa kamfanonin kasar Sin zuba jari a nahiyar Afirka. Zuwa yanzu, asusun yana da ofisoshinsa a kasashen Afirka ta Kudu, Habasha, Zambia, da Ghana, don haka ofishin Kenya ya kasance na 5 da asusun ya kafa a nahiyar Afirka.

A yayin bikin bude ofishin a Kenya, mista Chi Jianxin, babban darektan asusun CAD, ya bayyana cewa, kafa wannan ofishi zai taimakawa kamfanonin kasar Sin wajen habaka harkokinsu da kara zuba jari a kasashen Afirka daban daban.

Ya zuwa karshen watan Agustan bana, asusun CAD ya riga ya zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 3.5 don tallafawa manyan ayyuka 87 da ake gudanar da su a kasashe 36 dake nahiyar Afirka, wadanda suka shafi hadin gwiwa a fannin masana'antu, kayayyakin more rayuwa, hakar ma'adinai, aikin gona da dai makamantansu. Ta wadannan ayyuka, an samu damar amfanawa jama'ar kasashen Afirka da yawansu ya kai fiye da miliyan 1, tare da sa kaimi ga kamfanonin Sin da su kara zuba jari a Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China