in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta fara cin gajiyar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki
2016-09-05 11:14:26 cri

Wani masani a fannin tattalin arziki dan kasar Kenya Peter Kagwanja, ya ce hadin gwiwar da kasar sa ke yi da sauran sassan duniya ta fuskar diflomasiyyar tattalin arziki, ya fara haifarwa kasar da da mai ido.

Mr. Kagwanja wanda ke jagorantar wata cibiya ta bincike da tsare tsaren ci gaba a nahiyar Afirka dake birnin Nairobin kasar Kenya, ya yi wannan tsokaci ne cikin wata makala da wata jaridar kasar ta wallafa, yana mai cewa matsayin Kenya na wata mahada ta cinikayya, da zuba jari, da hada hadar sufuri a yankin gabashin Afirka ya kara samun bunkasa, sakamakon maida hankali da mahukuntan ta suka yi, wajen raya hadin gwiwar tattalin arziki da sauran sassan duniya.

Masanin ya kara da cewa, Kenya ta karkata akalar manufofin ta na kasashen waje, wajen inganta aikin soji, da fadada harkokin tattalin arziki, tare da samar da ci gaba a bangaren musayar al'adu, da harkokin zuba jari na kai tsaye a kasar.

A daya bangaren kuma, kasar ta zamo wani ginshiki na wanzar da zaman lafiya a yankin ta, a yayin da take kara fadada hadin gwiwa da sauran sassa a fannin inganta tattalin arziki da sauran kasashen duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China