Ranar 19 ga wata, shugaban Amurka Barack Obama ya yi jawabi dangane da fashewar abubuwa a birnin New York da jihar New Jersey da kuma lamarin jikkata mutane da wuka a jihar Minnesota, inda ya jaddada cewa, kasarsa ta Amurka ba za ta mika wuya ga tsoro ba, za ta kuma ci gaba da shugabantar kawancen kasa da kasa kan yaki da 'yan tawayen ISIS, da gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci.
A cikin jawabinsa a lokacin da yake halartar tarurukan babban taron MDD a wannan rana, Obama ya ce, yana sa kulawa sosai kan sabon ci gaba da aka samu wajen bin bahasin fashewar abubuwan a birnin New York da jihar New Jersey, kuma gwamnatin tarayya za ta bai wa mahukuntan birnin New York da jihar New Jersey dukkan taimakon da ya wajaba wajen bin bahasin abubuwan da suka faru. Ya kara da cewa, shirya babban taron MDD a ko wace shekara a birnin ya kan bai wa mahukuntan New York matsin lamba sosai ta fuskar tsaro, don haka wajibi ne gwamnatin tarayya ta yi iyakacin kokarin ba da tallafawa. Haka kuma za a kama wadanda suke da hannu kan fashewar tare da gurfanar da su a gaban kotu cikin hanzari. A sa'i daya kuma, shugaban Amurka ya yi fatan ganin cewa, kafofin yada labaru sun kai zuciya nesa yayin da suka ba da labari kan al'amura masu sarkakiya, kada su watsa labarun da ba su da tushe, ko kuma watsa labaru kan al'amuran ta bangare daya, ba bisa tushen binciken da mahukuntan suke gudanarwa ba.
Dangane da lamarin jikkata mutane da wuka a jihar Minnesota kuma, Obama ya ce, bincken da aka gudanar yanzu haka ya shaida cewa, lamarin ba shi da alaka da fashewar abubuwa a birnin New York da jihar New Jersey.
Ya sake nanata cewa, jami'an tsaro suna nan suna tabbatar da tsaron unguwanni a ko da yaushe. Kamata ya yi ko wane Ba'amurke ya sanar wa mahukuntan abun da ake tuhuma masa a kai.
Haka zalika, Obama ya jaddada cewa, kasarsa ta Amurka za ta ci gaba da jagorantar kawancen kasa da kasa na yaki da 'yan tawayen ISIS, da gudanar da ayyukan yaki da ta'addanci. Amurka ba za ta mika wuyanta ga tsoro ba.
A wannan rana da dare kuma, Obama zai gana da firaministan kasar Iraki Haider al-Abad, inda za su tuntubi juna kan ci gaban yaki. Sakamakon karbe yankuna da dama da ke hannun 'yan tawayen ISIS, hakan ya karya lagon 'yan tawayen na baza kiyayya a tsakanin al'umma, da kuma jan hankalin 'yan ta'adda a kasashen ketare ba.
A yayin da Obama yake ba da jawabin, kafofin yada labaru na Amurka sun labarta cewa, bangaren jihar New Jersey ya sanar da cewa, an kama Ahmad Khan Rahami a jihar, wanda ake zarginsa da sa hannu cikin fashewar abubuwan a birnin New York da jihar New Jersey. (Tasallah Yuan)




