A jiya ne aka kai wani harin kunar bakin wake da bama-bamai a unguwar 'yan Shia da ke birnin Baghdad, babban birnin kasar Iraki, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 7, a yayin da wasu mutane 28 kuma suka jikkata.
A wannan rana da dare, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai wannan farmaki, tana mai cewa, ta kai harin ne kan mabiya Badr da kuma 'yan Shia mai alaka da kasar Iran, kungiyar da ta yi kaurin suna a lokacin yakin kasar Iraki na shekarar 2003, wadda kuma ta taka muhimmiyar rawa a yaki da kungiyar IS.(Lami)




