Mataimakin darektan kwamitin kula da harkokin bunkasuwa da yin kwaskwarima na Sin, Ning Jizhe ya bayyana cewa, kawo yanzu baki daya jimillar jarin da Sin ta zuba a kasashen Afirka ta kai sama da dala biliyan 100, a yayin da kamfanonin Sin sama da 3100 suna zuba jari tare da gudanar da harkokinsu a kasashen Afirka. Bisa sakamakon da aka samu a taron koli na Johannesburg, hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannin masana'antu ya riga ya zama babban karfi na bunkasa masana'antun Afirka.
Shugaban hukumar sa kaimi ga zuba jari da fitar da kayayyaki zuwa ketare ta kasar Saliyo ya bayyana cewa, yadda kamfanonin Sin suke zuba jari ga kasashen Afirka ba ma kawai zai taimaka wa kasashen Afirka wajen kyautata karfin masa'anatunsu ba, har ma zai rarraba fasahohin kamfanonin Sin zuwa ga kasashen Afirka, ta yadda za su tabbatar da kirkire-kirkire.(Fatima)