Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, da shugaban kasar Benin Patrice Talon, da shugaban bankin duniya Kim Yong da tawagogin kasashen Afirka da hukumomin kasa da kasa da yankuna, da 'yan kasuwa daga kasashen daban-daban, da hukumomin da abin ya shafa da tawagogin larduna da biranen kasar Sin, gaba daya mutane fiye da 300 sun halarci dandalin tattaunawar.
Ma Kai ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, dandalin tattaunawa kan zuba jari a kasashen Afirka muhimmin dandali ne da zai kara taimakawa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, wanda ya dauki alhakin aiwatar da ayyukan da aka cimma a gun taron kolin FOCAC na birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Ta wannan taro za a bullo da sabbin hanyoyin zuba jari da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.
Shugaba Jacob Zuma, da Patrice Talon da Kim Yong sun bayyana cewa, gudanar da dandalin tattaunawar na wannan karo ya zo a lokacin da ya dace, ganin irin nasarar da taron kolin kungiyar G20 na birnin Hangzhou ya cimma tare da mayar da hankali ga bunkasuwar kasashen Afirka. An samu nasarori da dama kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kana ana kokarin ganin samun ci gaba a kasashen Afirka. (Zainab)