in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gwada kayayyakinta a bikin baje-kolin jiragen sama da aikin tsaron kasa na Afirka
2016-09-15 13:11:34 cri

A jiya Laraba aka bude taron baje-kolin jiragen sama da aikin tsaron kasa na Afirka karo na 9 a birnin Pretoria, fadar mulkin kasar Afirka ta Kudu. Hukumar masana'antu da fasaha da fuskar tsaron kasar Sin ta hada kai da kamfanonin cinikin soja na kasar Sin 8, don su halarci bikin baje-kolin tare, lamarin da ya jawo hankali sosai.

Bayan bude bikin baje-kolin, ministocin tsaron kasa na wasu kasashen Afirka, da sauran kusoshin rundunonin soja da gwamnatoci sun ziyarci yankin gwada kayayyaki da na'urori kirar kasar Sin, inda suka tattauna da ma'aikatan kasar Sin dangane da ingancin kayayyakin da dai sauransu, tare da bayyana fatansu na hada kai da kamfanonin kasar Sin.

Bugu da kari, sojojin kasashen Sin da Zambiya za su gwada jiragen sama masu ba da horo kirar L-15 da kasar Sin ta kera a yayin taron baje-kolin, lamarin da zai kasance karo na farko ne da irin wannan jirgin sama zai bayyana a idanun jama'a, bayan da kasar Sin ta mika shi a hannun sojan Zambiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China