Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, burin tsagerun Niger Delta dake fasa bututun mai a yankinsu, shi ne yi wa kasar mulkin mallaka ta fuskar tattalin arziki. (The Punch)
Ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank Walter Steinmeier, ya ce yawan jimillar kudaden cinikayya tsakanin kasarsa da Najeriya ya ragu da kaso 50 cikin dari, tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015. Steinmeir wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce adadin ya yi kasa daga Euro biliyan 5.4 a shekarar 2014 zuwa Euro biliyan 2.9 a shekarar bara.
Ministan na wannan tsokaci ne bayan kammalar taron dandalin hadin gwiwar wakilan kasashen biyu, inda ya bayyana rashin jin dadi game da aukuwar wannan koma-baya. (Daily Trust)
Babban alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Mahmud Mohammed, ya yi Allah wadai da kame wasu alkalan kotuna da hukumar tsaron farin kaya ta kasar DSS ta gudanar, yana mai cewa lamarin ya janyo matukar damuwa ga sashen shari'ar kasar. (The Guardian) (Saminu)