FAO ta bayyana a cikin rahoto mai taken "yanayin abinci da aikin gona na shekarar 2015" cewa, yawancin kasashen duniya suna da karfi wajen bada kariya ga mazauna karkara ciki har da kasashe mafi talauci. FAO ta yi hasashe cewa, idan aka zuba jari dala biliyan 67 ga aikin gona da mazauna karkara a kowace shekara, za a cimma burin kawar da talauci a shekarar 2030.
Rahoton ya yi nuni da cewa, hanyar bada kariya daga al'umma ga mazauna karkara ba za ta tabbatar da kawar da taulauci da yunwa a dogon lokaci ba, don haka akwai bukatar a hada kai da kuma daidaita jarin da ake zuba daga al'umma ga mazauna karkara da jarin da ake zuba daga gwamnati da masu zaman kansu ga aikin gona, ta yadda za a iya kawar da talauci a kauyuka ta hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa. (Zainab)