in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake zabar Jose Dasilva a matsayin shugaban hukumar UNFAO
2015-06-07 13:36:59 cri
A sake zabar Jose Graziano Dasilva a matsayin babban daraktan hukumar aikin gona da samar da abinci ta MDD ko UNFAO a takaice, wanda hakan ke nuna cewa Mr. Dasilva zai ci gaba da jagorantar hukumar har ya zuwa watan Yulin shekarar 2019.

An tabbatar da Mr. Dasilva a matsayin nasa ne yayin babban taron gudanarwa da hukumar ke yi bayan shekaru biyu-biyu.

Kasar Brazil ce ta gabatar da Mr. Dasilva, kuma shi ne dan takara daya tilo a zaben na bana. Bayan tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Dasilva ya jaddada cewa, hukumar UNFAO za ta yi iyakacin kokarinta wajen cika alkawarinta game da kawar da yunwa, da rashin abinci mai gina jiki.

Tun hawansa mukamin babban daraktan hukumar a shekarar 2012, Mr. Dasilva ya yi matukar kokari, wajen sauya tsarin ayyukan hukumar, cikin irin matakan da ya dauka hadda kara mai da hankali kan muhimman fannoni biyar, da suka hada da kawar da yunwa gaba daya, da dakile matsalar rashin nau'o'in abinci masu gina jiki. Bugu da kari, Mr. Dasilva ya maida hankali wajen kara hadin gwiwa da kasashen duniya, musamman a fannin neman goyon baya, da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China