in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayar da gagarumar gudummawa ga kasashe masu tasowa a fannin samar da abinci
2015-12-07 20:13:46 cri

Kasar Sin ta bayar da gagarumar gudummawa ga kasashe masu tasowa a fannin ci gaban ayyukan gona da samar da abinci bisa tsarin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, hakan ya sa ake fatan kasar Sin za ta kara yin tasiri a cikin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa a nan gaba.

Jong-Jin Kim, shugaban sashen kula da hadin kai da tattara albarkatu a tsakanin kasashe masu tasowa na kungiyar samar da abinci da aikin gona ta MDD wato FAO ya fadi haka ne yau Litinin a birnin Wuhan na kasar Sin, a yayin da yake jawabin a matsayinsa na wakilin kungiyar FAO.

Jong-Jin Kim ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce mai yawan al'umma, wadda ta ta'allaka ga ayyukan gona. A kullum aikin raya ayyukan gona da samar da abinci, aiki ne mai matukar kalubale. Amma kasar Sin ta warware wannan matsala bisa ci gaban fasahohin noma da kirkire-kirkire da ta samu, baya ga taimakawa kasashe masu tasowa na duniya da fasahohi wajen tinkarar matsalar karancin abinci, da kawar da kangin talauci, gami da neman samun dauwamammen ci gaban albarkatun noma.

Alkaluman kididdiga na nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yuni na bana, bisa tsarin hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa da kasar Sin ta gudanar tare da kungiyar FAO, kasar Sin ta tura kwararru 1023 zuwa kasashe da yankuna 25 da ke Afirka, Asiya, kudancin tekun Pasifik, Latin Amurka, da kuma Caribbean, wadanda yawansu ya kai kashi 56 cikin 100 na dukkan mutanen da ta tura karkashin wannan tsari. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China