in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe sojojin Somaliya 22 a wani hari da aka kai da wani jirgin saman Amurka maras matuki
2016-09-29 11:12:18 cri
Wani jami'in Somaliya ya bayyana a jiya Laraba cewa, wani jirgin saman kasar Amurka maras matuki ya kai hari kan yankin tsakiyar kasar, wanda ya haddasa mutuwar sojojin kasar 22, yayin da wasu 16 suka jikkata.

Ministan tsaro gwamnatin yankin Galmudug dake tsakiyar kasar Somaliya ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, a wannan rana jirgin saman Amurka maras matuki ya kai harin kan kungiyar Al Shabaab, amma harin ya haddasa mutuwar sojojin Somaliya da dama. Wannan danyen aiki ya haddasa zanga-zanga a kasar. Kuma ya kara da cewa, watakila sojojin Amurka sun sami sakon asiri bisa kuskure. Don haka kamata ya yi Amurka ta yi bayani kan wannan harin da ta kai.

Rahotanni na cewa, Amurka ta jibge wasu sojojinta a Somaliya, da zummar ba da jagoranci da tallafawa wajen yaki da kungiyar Al Shabaab. A kullum sojojin Amurka su kan kan farmaki da jirgin sama maras matuki kan kungiyar Al Shabaab.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China