Jiya Talata, gwamnatin Somaliya ta karbi Mista Stephen M. Schwartz a matsayin Jakadan Amurka a kasar a lokacin da ya kama aiki a ofishin jakadacin Amurka dake Somaliya. A wata sannawar da ministan harkokin waje na Somaliya ya fitar yana cewa, nada Schwartz dan shekaru 58 da haihuwa a matsayin jakadan Amurka da ke kasar, wata sabuwar hanya ce ta kara dankon dangantaka tsakanin kasashen biyu. Wannan shi ne karon farko da Amurka ta bude ofishin jakadacin a Somaliya tun daga shekarar 1991. Gamnatin Jamhuriyar Somaliya na neman hanyoyin karfafa dangantaka da hadin gwiwa tare da Amurka domin samun alfanu ga al'ummomin kasashen biyu. (Laouali Souleymane).