Cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, bisa sauyin iko tsakanin kasa da kasa, da kuma karuwar kalubalolin da ake fuskanta, kamata ya yi a karfafa gudanar da harkokin duniya bisa tsari, tare kuma da inganta gudanar da kwaskwarima kan tsarin wannan aiki. Ya ce bisa wannan yanayin da ake ciki, ya kamata a yi amfani da wannan dama, da nufin ciyar da bunkasuwar tsarin duniya gaba kuma yadda ya kamata, da kuma kara kiyaye moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, ciki har da kasar ta Sin. (Bilkisu)