Xi Jinping ya jaddada cewa, 'yan wasannin motsa jiki na kasar Sin sun yi namijin kokari kuma sun samu nasara sosai a yayin gasar wasan Olympics ta Rio, sun kuma nuna ruhun Olympics da ruhun al'ummar Sinawa a yayin da suke fafatawa a gasar.
Xi Jinping ya kuma nuna cewa, bunkasuwar wasannin motsa jiki wata muhimmiyar alama ce dake bayyana yadda ake bunkasa zaman al'umma da ci gaban bil Adama, kuma muhimmiyar alama ce dake nuna karfin kasa. Yana fatan za a yi kokarin samun nasarar shirya gasar wasan Olympics ta lokacin sanyi da za a yi a nan Beijing a shekarar 2022 domin ci gaba da bunkasa wasannin motsa jiki a kasar. (Sanusi Chen)