in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya bayar da jawabi a yayin taron murnar cika shekaru 65 da kafuwar majalisar CPPCC
2014-09-21 20:46:22 cri

A yau, ranar 21 ga wata, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar, CPPCC sun shirya taron murnar cika shekaru 65 da kafuwar majalisar a nan Beijing. A yayin taron, shugaban kasar, kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Xi Jinping ya bayar da wani muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a ta kasance tamkar wata muhimmiyar hanya ce da jama'a suke aiwatar da tsarin dimokuradiyya da kansu.

Mr. Xi ya kara da cewa, shimfida dimokuradiyya irin ta tsarin gurguzu ta hanyar yin shawarwari, salon musamman da kasar Sin ke amfani da shi a kokarin gudunar da harkokin siyasa irin na dimokuradiyya na tsarin gurguzu, haka kuma ta kasance wata muhimmiyar alamar da ke bayyana yadda jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin take sauraran ra'ayoyin jama'a a lokacin da take gudanar da harkokin siyasa. Bisa ka'idojin tsarin gurguzu da kasar Sin take bi, ana tattaunawa abubuwa kamar yadda ya kamata, ana kuma muhawara sosai tsakanin jama'a kan harkokin jama'a a kokarin neman matsaya daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China