in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nemi kasar Amurka da ta daina yin tsokana a yankin tekun kudancin kasar Sin
2015-05-27 20:00:34 cri
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a kwanan baya, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka ya jaddada cewa, bangaren Amurka zai ci gaba da daukar matakan bincike a yankunan dake kusa da tsibiran tekun kudancin kasar Sin domin tsaron 'yancin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa.

Game da wannan matsayin da bangaren Amurka ke dauka, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing, cewar matakin da kasar Amurka ta dauka na tura jiragen saman soja zuwa yankin tekun kudancin kasar Sin domin yin bincike kan tsibiran kasar Sin, zai iya ta da fitina cikin sauki. Sakamakon haka, bangaren Sin na fatan bangaren Amurka ya dauki matakan da suka kamata ya dauka na tabbatar da zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin, kuma ya kamata ya nazarci batutuwan da abin ya shafa kamar yadda ya dace, kuma dole ne ya guji aikata duk wasu matakai da maganganun da za su kasance masu hadari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China