in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar siyasa ta JKS ta nazarci makomar tattalin arzikin shekarar 2015
2014-12-05 20:27:50 cri
A yau Jumm'a 5 ga wata ne, hukumar siyasa ta jam'iyyar kwaminis JKS ta kasar Sin ta shirya taro, inda aka tattauna da kuma nazartar makomar tattalin arziki na shekarar 2015. Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS shi ne ya shugabanci taron.

A yayin taron, ana ganin cewa, a shekarar bana, tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin na samun ci gaban da ake fata. Sakamakon haka, yanzu ana cikin kyakkyawan hali ta fuskar tattalin arziki da zaman al'umma. A waje daya hannun kuma, ana ganin cewa, a yanayin da ake ta fuskar tattalin arziki, ana kuma fama da dimbin matsaloli da kalubale a fannoin tattalin arziki da zaman al'umma kamar yadda ya kamata.

Sannan, an nuna cewa, shekarar 2015 ita ce shekarar karshe ta kammala shirin shekaru biyar-biyar na 12 na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara yin kwaskwarima, kuma farkon shekara ce ta ingiza tafiyar da harkokin mulki bisa doka. Sakamakon haka, tana da muhimmanci sosai ga ci gaban tattalin arziki. Ana fatan za a ci gaba da mai da hankali kan inganta tattalin arziki da moriyar da za a samu bisa ka'idar neman ci gaba cikin hali mai dorewa, ta yadda za a kyautata tsarin tattalin arziki, da tabbatar da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China