in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ta shirya liyafar shiga sabuwar shekara
2014-12-31 16:53:26 cri
A safiyar yau Laraba 31 ga watan Disamba, kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ya shirya liyafar shiga sabuwar shekara a babban dakin majalisar, inda shugaba Xi Jinping ya halarta.

Shugaba Xi a cikin jawabin sa da ta karata, ya jaddada cewa, magance matsalolin da muke fuskanka zai taimaka ga ci gabansu, yayin da zuciyar jama'a ta fi muhimmanci a fannin siyasa. A kokarin sa kaimi ga ayyukan JKS da kasar Sin, dole ne a tsaya tsayin daka kan dora muhimmanci kan daidaita matsaloli da sauraron muryar jama'a.

Haka kuma, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin shekara mai karewa, sun taya murnar cika shekaru 65 da kafa majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ikon jama'a na ba da shawara kan harkokin siyasa, da mai da hankali kan yin nazari kan manyan batutuwa na yin kwaskwarima da samun bunkasuwa, da bayyana ra'ayin jama'a, da sa ido, ta yadda ta ba da babbar gudummawa wajen sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a kasa. A cikin sabuwar shekara mai zuwa, ya ce ya kamata a yi tsayin daka wajen kyautata tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa a karkashin jagorancin JKS, da hada zukatan jama'a da karfinsu wuri daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China