Mr Ban ya kuma bayyana a cikin wata sanarwa da kakakinsa ya rabawa manema labarai cewa, fara aiki da yarjejeniyar da duniya ta amince da ita, wata babbar nasara ce. Kuma wannan wata alama ce da ke nuna yadda ra'ayin kasashen duniya ya zo daya game da tunkarar matsalar sauyin yanayin duniya.
A don haka Ban Ki-moon ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su kara hada kai domin tunkarar kalubalen sauyin duniya.
Shafin yanar gizo na MDD mai kula da taro kan sauyin yanayi, ya sanar a jiya Laraba cewa, ya zuwa yanzu kimanin kasashen duniya 72 ne suka sanya hannun kan yarjejeniyar wadda aka cimma a watan Disamban shekarar 2015, inda aka yi kiyashin cewa,suna fitar da sama da kashi 56 cikin 100 na hayaki mai gurbata muhalli.(Ibrahim)