in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labaran Najeriya(161010)
2016-10-10 19:43:24 cri

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana kamen wasu manyan alkalai da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gudanar, a matsayin wani mataki na yaki da cin hanci da rashawa, amma ba wai barazana ga sashen shari'ar kasar ba.

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriyar Garba Shehu ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar a jiya Lahadi. (Daily Trust)

Babban bankin Najeriya CBN ya ce, nan gaba kadan, za a kai ga cimma nasarar aiwatar da tsarin nan na musayar kudin Najeriya Naira da Yuan na kasar Sin, matakin da zai rage matukar bukatar da ake da ita ga dalar Amurka.

Gwamnan bankin na CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan, yayin taron shekara-shekara na hadin gwiwar bankin duniya da asusun ba da lamuni na IMF, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Washington DC. (The Guardian)

Kamfanin samar da lantarki a Najeriya TCN, ya ce karfin lantarkin da kasar ke samu ya ragu daga megawatt 4,000 a ranar Asabar, zuwa megawatt 3,568 a ranar Lahadi. (Vanguard) (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China