Shekaru da dama da suka wuce, an sha gabatar da matakan yaki da cutar ta Maleriya a matakai na kasa da kasa a Najeriyar, to sai dai a wannan karo, gwamnatin ta ce matakan da take shirin dauka za su kawar da cutar ne kwacokan a fadin kasar.
Gwamnatin Najeriyar tace, ta bullo da shirin kawar da cutar Maleriyar wanda aka tsara shi ta yadda kwayoyin cutar ba za su taba yin tasiri ba a jikin bil adama a duk fadin kasar.
A cewar Patricia Uhomoibhi, babban jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar, dabarun da aka bullo dasu zasu maida hankali ne, wajen daukar matakan farko da kawar da cutar nan da sheklara ta 2020, da kuma kawo karshen hasarar rayukan da ake samu a sanadiyyar cutar nan da shekarar ta 2020.(Ahmad Fagam)