Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari tare da shugaban majalisar gudanarwar kasar Cuba kuma shugaban taron ministocin kasar Raúl Castrol a birnin Havana a yammacin ranar 24 ga wannan wata.
A gun shawarwarin, Li Keqiang ya bayyana cewa, a cikin shekaru 56 da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Cuba, ana samun babban ci gaba kan raya dangantakarsu. Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar sada zumunta a tsakaninta da kasar Cuba, da nuna goyon baya ga kasar Cuba wajen bin hanyar tsarin gurguzu, da sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, Castrol ya bayyana cewa, kasar Cuba ta nuna amincewa ga shawarar da Sin ta bayar wajen sa kaimi ga raya dangantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Cuba, kana tana son koyi da fasahohin Sin yayin da take raya kasar, da kiyaye yin mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a kan harkokin kasa da kasa yayin da suke yin kokarin amfanawa jama'arsu, da kuma kiyaye moriya guda irinta kasashe masu tasowa. (Zainab)