A yayin ganawar, firaminista Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Cuba suna da zumunci mai tarihi, kuma suna ta nuna amincewar juna a fannin siyasa, a yanzu haka kuma suna karfafa hakikanin hadin kai a fannoni daban daban. A cewar mista Li, yana fata a yayin ziyararsa zai yi cudanya sosai tare da shugabannin kasar Cuba kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma wasu batutuwan dake jawo hankulansu duka, tare kuma da yin mu'ammala kan shirin raya kasashen biyu da hakikanin hadin kai a tsakanin kasashen biyu, da nufin ciyar da bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu da hadin kansu gaba, ta yadda za a kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu.
A nasa bangare, Mario Diaz-Canel Bermudez ya amince da yabo da firaminista Li ya nuna game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya bayyana cewa, ziyarar firaminista Li na da ma'ana sosai, za ta inganta dangantakar dake tsakanin Cuba da Sin, da kuma sha'anin raya kasashen biyu. A cewarsa, yanzu kasar Cuba na kokarin kyautata tsarin tattalin arziki, yana fata kasar Sin za ta ci gaba da shiga ayyukan raya tattalin arziki da al'ummar kasar ta Cuba. A karshe dai ya bayyana fatansa na cimma nasara game da ziyarar firaminista Li.
Uwargidan firaminista Li madam Cheng Hong ita ma ta halarci wannan ganawar tsakanin manyan jami'an biyu. (Bilkisu)