Za a kaddamar da bikin bude taron ministoci karo na biyar, na dandalin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashe masu magana da harshen Portugal a birnin Macau na kasar Sin, a ranar 11 ga watan nan.
Bikin zai samu halartar firaministan kasar Sin Li Keqiang, da takwaransa na kasar Portugal Antonio Costa, da na kasar Cape Verde Ulisses Correia Silva, da na kasar Guinea-Bissau Baciro Dja, da na kasar Mozambique Carlos Agostinho do Rosario. Kana da wakilan gwamnatocin kasashen Brazil, da Angola, da Timor-Leste su ma za su halarci taron.
A yayin taron, firaminista Li Keqiang zai gabatar da jawabi, zai kuma ganawa da wasu shugabannin kasashe da za su halarci taron.(Kande Gao)