Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana kudurinsa na goyon bayan dokokin yankin musamman na Macao na kasar Sin.
Mr. Li ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a ganawarsa da jagoran yankin Chui Sai On yayin wata ziyarar gani-ido ta kwanaki uku da ya fara a yankin.
Firaminista Li ya ce, yanzu haka an samu muhimman ci gaba a fannonin siyasa, tattalin arziki da zaman jituwa tsakanin al'ummomin yankin, tun bayan da yankin na Macao ya dawo karkashin ikon kasar Sin kimanin sama da shekaru 17. Matakin da ke nuna nasarar da aka samu a gwajin da ake yi na tsarin kasa daya, mai bin tsarin mulki iri biyu.
Haka kuma, tattalin arzikin yankin na Macao ya fuskanci sanye-sauye a cikin shekaru biyu da suka gabata. Kana gwamnatin yankin ta yi nasarar magance matsalolin da bangarorin rayuwar al'ummar yankin su ke fuskanta baya ga wasu sabbin nasarori da aka samu.
Firaminista Li ya bayyana cewa, yana fatan mahukuntan yankin, za su ci gaba da gina yankin a matsayin wurin yawon shakatawa da ke kan gaba a duniya, cibiyar jin dadi da kuma wani wuri na ba da hidima a bangaren hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen da ke magana da harshen Portuguese.
Ana sa ran Firaminista Li zai halarci bikin bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar tattalin arzikin da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen da ke magana da harshen Portuguese.(Ibrahim)