Haka kuma, a ranar 22 ga watan nan da muke ciki, hukumar zaben tarayyar kasar Somaliya ta taba fidda wata sanarwar cewa, a halin yanzu, ana fuskantar kalubaloli da dama wajen gudanar da zabe a fannonin siyasa, kudaden gudanar da zabubbuka da kuma tsaro da dai sauransu.
Haka zalika, akasarin ra'ayoyin jama'a suna ganin cewa, mai iyuwa ne jinkirin gudanar da zaben majalisar wakilai da majalisar dattijai zai sa ba za a iya gudanar da babban zaben shugaban kasar da aka tsara gudanarwa a ran 30 ga watan Oktoba mai zuwa ba.
A ran 4 ga watan nan da muke ciki ne, fadar shugaban kasar Somaliya ta sanar da umurnin cewa, shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud ba zai iya gudanar da ayyukan shugaban kasa ba daga ran 10 ga watan Satumba, watau lokacin da ya kammala wa'adin aikinsa, kana, bisa umurin da ta fidda, za a iya tsawaita wa'adin aikinsa har zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba. (Maryam)