in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Somaliya ta yi kashedi kan duk wani jinkiri a cikin zabuka
2016-09-23 10:41:04 cri

Hukumomin zabe a Somaliya sun yi kashedi a ranar Alhamis cewa zabuka za su iya samun jinkiri dalilin wasu matsalolin kudi da na kalubalolin siyasa.

Hukumar tarayya da ta aiwatar da zabuka ba na kai tsaye ba (FIEIT) ta bayyana a cikin wata sanarwa a Mogadishu cewa za ta kira wani taro tare da shugabannin tawagogin zabuka na jihohin tarayya a ranar Jumma'a domin lalubo bakin zaren kalubalolin da ake fuskanta a yayin da kasar ke shirin gudanar da zabuka a ranar Asabar.

Hukumar zaben ta sanar a cikin watan Augusta cewa zabukan kananan 'yan majalisu za su gudana a ranar 24 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba, kana zabuka 'yan majalisar dattawa za su dauki yini guda kuma za'a gudanar da su a ranar 25 ga watan Satumba.

Amma duk da haka, FIEIT ta kuma bayyana cewa tana fama da kalubaloli na siyasa da na tsaro, a cewarta ba tare da wani karin haske ba. Shugabannin dake kula da zaben wakilai har yanzu ba su gabatar da takardar jerin sunayensu ta karshe ba, alhali kuma kwanaki biyu suke rage a gudanar da zabuka, in ji hukumar zaben.

Sanarwar ta biyo bayan wani sakon gamayyar kasa da kasa kan Somaliya inda aka bukaci ganin an gudanar da zabuka bisa lokacin da aka tsaida.

Wata sanarwa da aka fitar bayan wani zaman taro na manyan jami'ai kan Somaliya a dabra da babban taron MDD a ranar Laraba, ta yi kira ga Somaliya da ta sanya himma wajen ganin zabuka sun gudana ba tare da wani jinkiri ba.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China