in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci karin tallafi a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya
2016-10-11 13:14:07 cri

Mataimakin sakatare janar na MDD mai kula da shirin wanzar da zaman lafiya Herve Ladsous, ya bukaci kasashen duniya da su ci gaba da tallafawa yunkurin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Ladsous, ya yi karin haske ga kwamitin tsaro na MDD game da halin da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ke ciki, ya bayyana cewa, har yanzu akwai fargaba sakamakon zaman tankiya da ake cigaba da fuskanta a kasar, kuma har yanzu masu ta da zaune-tsaye suna nan da karfinsu.

Duk da irin cigaba da aka samu a halin yanzu, ya ce dole ne hukumomin kasar su tashi tsaye wajen karfafa hanyoyin da za su tabbatar da hadin kan kasa, da inganta sha'anin tsaro a kasar baki daya.

Ya jaddada muhimmancin cigaba da bada tallafi na kasa da kasa ga al'ummar kasar domin a samu zama lafiya mai dorewa.

Game da wannan batu, ya bukaci kwamitin tsaron MDD da ya nemi agaji daga mambobin kasashen domin tallafawa kasar gabanin taron neman tallafin da za'a gudanar a birnin Brussels a watan Nuwamba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China