Hukumar zaben kasar wanda ta bayyana haka a jiya Asabar ta ce Touadera ya samu kashi 62.71 cikin 100 na kuri'un da aka kada.
Touadera dan shekaru 58 ya taba zama mataimakin shugaban jami'ar Bangui, kana ya yi aiki a matsayin firaministan kasar a zamanin Francois Bozize daga shekarar 2008 zuwa 2013.
A wani labarin kuma, abokin takararsa a zaben shugabancin kasar Anicet-Georges Dologuele ya ce, zai mutunta sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar ta sanar. Dologuele ya ce, ya yi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar ta fitar yana nuna cewa, tsohon firaminista Dologuele ya samu kashi 37.29 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben na ranar 14 ga watan Fabarairu.
Jamhuriyar Afirka ta tsakiya dai tana kokarin bude wani sabon babi ne, bayan shafe shekaru 3 tana fuskantar tashin hankali tun lokacin da tsohon shugaban 'yan tawayen Seleka Micheal Djotodia ya hambarar da Francois Bozize daga karagar mulkin kasar.(Ibrahim)