in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CAR: An yi musanyar wuta tsakanin dakarun MDD da wata kungiya mai dauke da makamai a Bangui
2016-06-21 13:09:54 cri
Wani kazamin fada ya barka a ranar Litinin da yamma tsakanin sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Afrika ta Tsakiya (MINUSCA) da wata kungiyar dake dauke da makamai a Bangui, bayan garkuwa da 'yan sanda shida a ranar Asabar a babban birnin na Afrika ta Tsakiya.

A cikin daren Asabar zuwa Lahadi, 'yan sanda dake sintiri sun fuskanci wani hari da manyan makamai da wani gungun mutane da ba a tantance su ba ya kai musu a birnin, da ya koma wani fagen daga a lokacin rikicin da ya biyo karbe ikon tsoffin 'yan tawayen Seleka da shugabansu Michel Djotodia a ranar 24 ga watan Maris din shekarar 2013 daga hannun gwamnatin Francois Bozize.

A cewar 'yan sanda, gungun na kusa da tsoffin 'yan tawaye dake cigaba kasancewa, tare da abokan gabarsu da mayankan Anti-Balaka da ma sauran kungiyoyin siyasa da soja, wata barazana ga dawowar zaman lafiya da tsaro a cikin wannan kasa mafi talauci dake tsakiyar nahiyar Afrika.

An yi garkuwa da 'yan sanda shida a yayin wannan hari, a cewar majiyoyin 'yan sanda, da suka tabbatar da cewa akwai yiyuwar harin an kai shi domin mayar da maratani kan cafke wani gungun mayakan fulani dake rike makaman yaki goma sha biyu da suka hada Kalachnikovs a wannan yanki a daren Jumma'a.

A ranar Litinin, wani rukunin sojojin Bangaladech na tawagar MINUSCA ya isa yankin musulmin da kuma cibiyar tsoffin 'yan tawayen Seleka domin yunkurin kwato mutanen da aka yi garkuwa da su, a cewar majiyoyin 'yan sanda.

Yunkurin ya janyo wani kazamin fada tsakanin bangarorin biyu, inda sojojin MINUSCA hudu suka jikkata tare da mutuwar wasu da dama daga bangaren maharan, a cewar wani adadin wucin gadi da majiyoyin 'yan sandar suka bayar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China