Kotun wadda ta bayyana hakan a birnin Bangui a jiya Talata, ta kuma bayyana cewa, an gudanar da zaben shugaban kasar Afirka ta Tsakiya zagaye na biyu ne a ranar 14 ga watan Febrairu, kuma hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon sa a ranar 20 ga watan Febrairu. Bisa kididdigar da aka yi a matakin farko, Touadéra ya samu kuri'u kaso 62.71 cikin dari, don haka ya zama sabon shugaban kasar.
A shekarun baya baya nan, ana samun tashe-tashen hankula a kasar Afirka ta Tsakiya, inda fararen hula da dama suka rasa gidajensu. Don haka ake daukar zaben shugaban kasar na wannan karo a matsayin muhimmin mataki, na shimfida zaman lafiya a kasar. (Zainab)