A yayin bikin rantsar da shi, mista Touadera ya ce kasar Afrika ta Tsakiya za ta bude wani sabon babi bayan rikici.
Sabon shugaban kasar ya alkawarta gina wata kasa mai zaman lafiya, cikin hadin kai da cigaba. Domin cimma wannan buri ne kasar za ta kara karfafa tsaro da kwanciyar hankali. A bangaren tattalin arziki, mista Touadera ya bayyana zai aiwatar da sauye sauye kan harkokin kudi, kuma za'a karfafa cigaban kanana da matsakaitan masana'antu. (Maman Ada)