in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Sin da na Najeriya sun jagoranci bikin taya murnar kulla dangantaka tsakanin sassan biyu
2016-04-13 15:39:00 cri
A yau Laraba ne ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama, suka jagoranci bikin murnar cika shekaru 45 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashe biyu, a wani bikin da ya gudana a nan birnin Beijing.

Cikin jawabin da ya gabatar a yayin bikin, Mr Onyeama ya ce alakar Najeriya na dada bunkasa cikin wadannan shekaru, yayin da cinikayya tsakanin sassan biyu ta yi matukar fadada. Ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ware wasu sassan da gwamnatinsa za ta fi baiwa muhimmanci wajen inganta rayuwar al'ummar Najeriya, sassan da suka kunshi tsaro, da samar da ayyukan yi, da kuma yaki da fatara.

Ya ce a wannan gaba da aka kulla sabbin yarjejeniyoyi tsakanin sassan biyu, Najeriya za ta yi matukar cin moriya daga tallafin kasar Sin a fannoni da dama, ciki hadda bunkasa harkar noma, da kiwo, da raya masana'antu da kuma ba da horon kwarewa.

Daga nan sai ya godewa mahukuntan kasar Sin, bisa tarba ta musamman da suka yiwa tawagar shugaban na Najeriya, da kuma kwazon su wajen tabbatar da nasarar wannan ziyara.

Tun da farko a nasa tsokaci, Mr. Wang Yi cewa ya yi yana maraba da zuwan tawagar shugaban Najeriya kasar Sin mai kunshe da takwaransa. Ya ce ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a jiya, ta ba da damar daga matsayin dangantakar sassan biyu zuwa wani matsayi na koli, wanda kuma hakan ya share fagen ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen.

Ya ce shi da takwaransa na Najeriya sun tattauna a wannan rana, domin warware batutuwa dalla-dalla, don tabbatar da nasarar ayyukan da yarjejeniyoyin da aka kulla.

Daga nan sai ya yi fatan cewa bisa matakan da shugaban Najeriya ke dauka a yanzu haka, Najeriyar za ta kai ga kawo karshen manyan matsalolinta, ta kuma samu irin ci gaban da ya dace tsakanin sauran sassan kasashen Afirka.

Mr. Wang ya ce sassan biyu za su yi hadin gwiwa a fannonin da suka hada da na noma, da samar da manyan ababen more rayuwa, da sha'anin samar da kayayyaki, da kimiyya da fasaha musamman ta bincike da cin gajiyar ilimin kimiyyar sararin samaniya da dai sauran su.

Daga karshe Mr. Wang ya ce a wannan gaba da ake gudanar da wannan biki, yana fatan ci gaba da bunkasa cudanya tsakanin kasar Sin da Najeriya, tare da fatan samun makoma mai haske ga kasashen biyu. (Saminu, Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China