Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Aliyu Usman wanda ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya ce, 'yan bindigar ba su taba direban nasu ba. Ya ce, jami'ansu na daukar dukkan matakan da suka wajaba don tabbatar da cewa,an kubutar da mutanen biyu.
A halin da ake ciki yanzu,'yan bindigar sun tuntubi iyalan ministar, inda suka bukaci a ba su naira miliyan 10 kimanin dala 32,000 a matsayin kudin fansa kafin su saki ministar da kuma mijin nata.(Ibrahim)