A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Legas, kwamishinan lafiya na jihar Borno Haruna Msheila ya bayyana cewa, jiihar Borno ta yi maraba da shirin samar da horo ga ma'aikatanta, game da matakan gano cututtuka da daukar matakan da suka dace.
Msheila ya ce, shirin zai taimaka wajen daukar matakan da suka dace na rage mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.
Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan shawarar da hukumar lafiya ta duniya ta yanke na kara taimakon da ta ke bayarwa a fannin taimakon jin kai a jihar Borno da sauran jihohi uku da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Shirin na EWARS dai, tsari ne da aka bullo da shi da nufin sanya ido kan cututtuka, alamun gargadi da daukar matakan gaggauwa bayan gano bullar cututtuka a yayin da jama'a ke cikin wani yanayi na jin kai.(Ibrahim)