Tun dai bayan kammala hutun su a kwanan baya, 'yan majalissun dokokin Najeriyar ke daukar matakan da suke fatan za su tallafa, wajen fidda kasar daga halin koma bayan tattalin arziki da take fama da shi. Tuni kuma 'yan majalisar dattijan Najeriyar suka bayyana aniyar gudanar da wani taro na yini biyu domin tattauna wannan matsala.
Tattalin arzikin Najeriya ya fada mawuyacin hali a hukunce, tun bayan da ma'aunin GDPn kasar ya yi kasa da kaso 2.06 bisa dari, a watanni 3 na biyu na shekarar bana, bayan da GDPn na yi kasa da kaso 0.36 a watanni 3 na farkon shekarar.(Saminu Alhassan)