in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada muhimmancin martaba ka'idojin kiyaye muhallin duniya
2016-08-24 20:21:23 cri
A kwanan baya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a lokacin da yake rangadin aiki a lardin Qinghai dake yammacin kasar Sin, cewar kare muhalli da kuma bunkasa harkokin kare duniyarmu, shi ne abu mafi muhimmanci ga kokarin bunkasuwar kasar Sin ba tare da tangada ba. Abu mafi daraja a lardin Qinghai shi ne yanayin muhallin yankin mai inganci. Sakamakon haka, babban nauyin da aka dora wa jama'ar lardin shi ne bunkasa harkokin kare muhalli, a matsayin wani babban jigon kare muhallin kasar Sin, ta yadda za a iya cimma burin samun daidaito tsakanin moriyar tattalin arziki da zaman al'umma ta hanyar kare ingancin muhallin duniyarmu.

Daga ranakun 22 zuwa 24 ga wannan watan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a wasu yankunan lardin Qinghai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China