Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya nuna juyayi kwarai ga iyalan wadanda suka rasu da kuma gwamnatin kasar, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Kaza lika, Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamnatin jamhuriyar ta Nijar da ta gaggauta gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi gaban kuliya, a kuma karfafa matakan tsaro da ake samarwa a sansanonin 'yan gudun hijira da sauran wuraren da a kan kai wa hare-hare.
Wasu kafofin watsa labaran kasar dai sun bayyana cewa, wasu dakaru ne suka kaddamar da harin kan sansanin 'yan gudun hijirar kasar Mali, dake arewa maso yammacin jamhuriyar Nijar a ranar 6 ga wata, lamarin da ya haddasa rasuwar sojojin kasar Nijar su a kalla 22, wadanda suke tsaron sansanin.
Bayan aukuwar wannan hari, rundunar sojan Nijar din ta tura karin sojojin kasa da na sama, domin zakulo dakarun da suka kai harin, kuma mai iyuwa wadannan dakaru wani bangare ne na 'yan ta'addan dake arewacin kasar ta Mali. (Maryam)