Firaministan kasar Sin mista Li Keqiang ya halarci liyafar da kulob din tattalin arziki ta birnin New York, da kwamitin kasar Amurka mai kula da huldar dake tsakanin Sin da Amurka, da kwamitin kasar mai kula da cinakayyar da ake yi tsakanin Sin da Amurka, suka shirya masa a daren ranar 20 ga wata bisa agogon wurin, inda ya yi jawabi na musamman dangane da yanayin tattalin arzikin kasar Sin.
A cewar firaministan kasar Sin, yanzu haka tattalin arzikin duniya bai farfado sosai ba, kana ana samun tashin hankali a kai a kai a wurare daban daban. Bisa wannan yanayi na rashin tabbas da kwanciyar hankali da ake ciki a duniyarmu, bai kamata ba a bar wata kasa ta kula da ita kanta kadai ba. Tsarin tattalin arzikin kasar Sin da na duk duniya a hade suke. Duk da cewa saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya dan ragu, amma har yanzu yana samun ci gaba ba tare da gamuwa da wata matsala ba. A farkon watanni 6 na bana, saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya kai kashi 6.7%, hakan ba wani karamin ci gaba ba ta la'akari da adadin tattalin arzikin Sin wanda ya kai dalar Amurka biliyan dubu 10.
Firaministan kasar Sin ya jaddada cewa, kasar Amurka ita ce mafi girma tsakanin kasashe masu sukuni, yayin da kasar Sin ta kasance kasa mafi girma dake kan hanyar tasowa. Akwai hanya mai nisa gaban kasar Sin kafin ta samu damar zamanintar da al'ummarta gaba daya. A cewar firaministan, ci gaban kasar Sin na dogaro kan samun zaman lafiya a duniya, da zaman jituwa tare da kasashe makwabta. Saboda haka kasar za ta tsaya kan manufar samun ci gaba cikin lumana, da kare ka'idojin kundin MDD, da rufawa majalisar baya yayin da take kokarin daidaita al'amuran duniya. Kasar Sin, in ji firaministan, na son hadin gwiwa tare da kasashe daban daban na duniya, don ciyar da tattalin arzikin duniya gaba, da samar da wani yanayi na girmama juna, da amfanawa juna.
Cikin shekaru 24 da suka wuce, kasar Sin ta dade tana kan matsayin kasa mai tasowa wadda ta janyo mafi yawan jarin kasashen waje. Kuma har yanzu tana da karfi sosai wajen janyo jarin waje. Kuma duk da haka kasar za ta kara bude kofa, da saukaka ka'idojin da aka tsara domin masu neman zuba jari a kasar ta Sin, in ji firaministan kasar.(Bello Wang)