in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya soma ziyarar aiki a Canada
2016-09-22 09:08:09 cri

Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Canada Justin Trudeau ya yi masa, a yammacin jiya ranar 21 ga wata bisa agogon wurin, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa filin jiragen sama na Ottawa Macdonald-Cartier, don fara ziyarar aiki a Canada.

A yayin da yake jawabi a filin jiragen sama, mista Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Canada suna da dangantaka mai inganci, kuma huldar dake tsakaninsu tana da makoma mai kyau, yanzu kuma dangantakar dake tsakaninsu na fuskantar muhimmiyar damar samun ci gaba. Firaministocin kasashen biyu sun kai ziyarar aiki ga juna a cikin wata guda, wannan ya nuna cewa, bangarorin biyu na mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninsu. A yayin wannan ziyarar, za a soma gudanar da tattaunawar shekara-shekara tsakanin firaministocin kasashen biyu, kana za a karfafa yin mu'ammala tare da bangaren Canada kan wasu batutuwan dake jawo hankulan bangarorin biyu, tare kuma da inganta yin cudanya da hadin kai a fannoni daban daban, da nufin ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Canada gaba.

A yayin ziyararsa a Ottawa, mista Li da takwaransa na Canada Justin Trudeau za su shirya tattaunawar shekara-shekara karo na farko tsakanin firaministocin kasashen biyu, da kuma sa ido kan cimma wasu yarjejeniyoyin hadin kai tsakanin bangarorin biyu. Baya ga haka, mista Li zai gana da babban gwamna, shugaban majalisar dattawan kasar, shugaban majalisar wakilai da kuma wasu shugabanni na kananan hukumomi na kasar ta Canada. Ban da wannan kuma, firaministocin kasashen biyu za su halarci dandalin tattaunawar hadin kai ta fannonin tattalin arziki da cinikayya da za a shirya a Montreal, tare kuma da yin jawabi a kai, kana za su halarci wasu bukukuwan al'adu da dai sauransu. (Bilkisu)
 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China