A jiya Alhamis da safe agogon kasar Canada ne firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na kasar Canada Justin Trudeau suka gana da manema labarai tare bayan da suka kammala shawarwari a tsakaninsu. Inda suka gabatar da sakamakon shawarwarinsu, tare da jinjinawa juna cewa, sun cimma nasarori da dama a yayin shawarwarin da suka yi cikin sahihanci.
Li Keqiang ya bayyana cewa, a yayin ziyararsa, an kaddamar da tsarin tattaunawa na shekara shekara na firaministocin kasashen Sin da Canada, wanda ya sheda kara kyautatuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren kuma, Mr. Trudeau ya ce, bangarorin biyu suna nacewa ga girmamawa juna, da kara tuntubar shugabanninsu, kana da kiyaye ci gaban dangantakarsu yadda ya kamata, wanda ya dace da moriyarsu bai daya. Ya kamata Canada da Sin su inganta hadin da ke tsakaninsu bisa ra'ayin nuna wa juna sahihanci, a kokarin kyautata cinikayya a tsakaninsu da kuma warware matsalolin da ke gabansu yadda ya kamata. (Kande Gao)