Ministan watsa labarai da al'adun kasar Lai Mohammed shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa gwamnati ba ta rufe kofofinta na tattaunawa da nufin kwato 'yan matan da aka sace ba, sabanin rahotannin akasin haka da wasu kafofin watsa labarai ke yayatawa.
Ministan ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa,gwamnati tana aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa,an sako 'yan matan daga hannun kungiyar ta Boko Haram.
A cewarsa, sau uku gwamnati tana bullo da matakan tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram don ganin an saki yaran ta hanyar musaya da mayakan kungiyar da ake tsare da su, amma hakan bai kai ga nasara ba.
A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne aka sace 'yan matan a dakunan kwanan marakantansu da ke garin Chibok a jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.(Ibrahim)