in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila ne Sin za ta kasance kasa daya tilo dake da tashar sararin samaniya nan da shekarar 2024
2016-10-08 12:26:36 cri

Shugaban rukunin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin Lei Fanpei, ya bayyana a taron ranar cika shekaru 60 da aka fara gudanar da aikin sararin samaniya na kasar Sin cewa, kasar Sin ta shirya harba babban sashen kumbon kwaji na tashar sararin samaniya a shekarar 2018. Sa'an nan za ta harba na'urorin tashar sararin samaniya da za ta kunshi sassa da dama da nauyin su ya kai tan 20 a shekarar 2022, matakin da zai ba da damar nan zuwa shekarar 2024, watau lokacin da tashar sararin samaniyar kasa da kasar za ta kare wa'adin ta, kasar ta Sin za ta kasance kasa daya tilo dake da tashar sararin samaniya.

Haka kuma, mataimakin shugaban sashen aikin sararin samaniya mai dauke da mutane Yang Liwei, ya ce, kasar Sin tana fatan habaka hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasashen duniya bisa fannonin tsara daftari, da nazari kan kayayyakin da suka shafi hakan, da ba da horo ga 'yan sama jannati da dai sauransu, domin raya ayyukan tashar sararin samaniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China