Bazoum ya shedawa manema labaru bayan kammala taron tattaunawa da takwaransa na kasar Algeriya Noureddin Bedoui cewar, kasashen nasu da sauran kasashen dake makwabtaka da su na cikin mawuyacin hali sakamakon matsalolin dake addabar su da suka hada da matsalar ta'addanci, da rashin zaman lafiya da ya tabarbare musamman a kasashen Libya, da rashin tsaro musamman a kasar Mali.
Domin tunkarar halin da ake ciki, Bazoum ya fada cewar, lokaci ya yi da da kasashen za su tattauna da juna game da batutuwan da suka shafi tsaro, domin daukar matakan da za su kawo maslaha wajen shawo kan matsalolin dake addabar kasashen ta hanyar kyakkyawan hadin kai.
Game da batun barazanar ta'addanci da safarar haramtattun kwayoyi, da matsalar bakin haure, kasashen biyu sun fara tsara wasu dabaru na hulda tsakaninsu, da kuma wasu kasashe da dama, da suka hada da kasashen Aljeriya, da Nijer, da Mali, da Chadi, da kuma Mauritaniya. (Ahmad Fagam)