Shugaba Issoufou ya bayyana cewa, ya halarci bikin kammala gina asibiti dake da gadaje 500 bisa taimakon kasar Sin ta bai wa Nijer a ranar 2 ga wannan wata, kana ya ziyarci babban ginin asibitin mai dauke da na'urorin aikin kiwon lafiya na zamani, ya nuna gamsuwa ga aikin, sannan ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta.
A nasa bangare, jakada Shi, ya bayyana cewa, wannan asibiti ya kasance asibiti mafi girma da kasar Sin ta taimakawa kasashen waje wajen ginawa, wanda ya sheda matukar muhimmancin da gwamnatin Sin ke dora ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Sin tana son yin kokari tare da Jamhuriyar Nijer wajen gudanar da ayyukan asibitin da bada jinya ga jama'ar kasar Nijer yadda ya kamata. (Zainab)